Lahadi 6 Satumba 2026 - 20:57
Ayoyin Rayuwa | Gargadin Alƙur’ani ga Masu Amfani da Shafukan Sada Zumunta

Hauza/ A cikin addinin Musulunci, duk wata magana ko aiki da ke haifar da yaɗuwar zunubi da munanan abubuwa a cikin al’umma abin zargi ne; domin hakan na iya sa munin zunubi ya gushe a zukatan mutane da dama, har ya zama wani abu na yau da kullum a cikin al’umma.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza | Yaɗa alfasha na daga cikin zunubban da aka tsananta yin gargaɗi a kansu. Alƙur’ani mai girma ya ce:

«إِنَّ الَّذِینَ یُحِبُّونَ أَنْ تَشِیعَ الْفَاحِشَةُ فِی الَّذِینَ آمَنُوا لَهُمْ عَذَابٌ أَلِیمٌ فِی الدُّنْیَا وَالْآخِرَةِ وَاللَّهُ یَعْلَمُ وَأَنْتُمْ لَا تَعْلَمُونَ.» ¹

“Lallai waɗanda suke son alfasha ta yaɗu a tsakanin muminai, suna da azaba mai raɗaɗi a duniya da Lahira; kuma Allah Ya sani, ku kuma ba ku sani ba.”

Ƙarin Bayani:

A cikin addinin Musulunci, duk wata magana ko aiki da zai haifar da yaɗuwar zunubi da munanan abubuwa a cikin al’umma abin zargi ne; domin hakan na iya sa mutane da dama su daina ganin zunubi a matsayin mummunan abu, har ya zama wani abu na yau da kullum a cikin al’umma.

Duba ga wannan riwaya ana iya bayyana mana muhimmanci da kuma tsananin wannan batu.

Wani mutum ya je wurin Imam Musa Al-Kazim (A.S) ya ce: “Raina fansarka, na ji wani labari game da ɗaya daga cikin ’yan’uwana wanda bai dace da shi ba. Na tambaye shi da kansa, sai ya musanta, alhali wasu amintattun mutane ne suka sanar da ni wannan labari.”

Imam (A.S) ya amsa da cewa:

«یَا مُحَمَّدُ کَذِّبْ سَمْعَکَ وَ بَصَرَکَ عَنْ أَخِیکَ فَإِنْ شَهِدَ عِنْدَکَ خَمْسُونَ قَسَامَةً وَ قَالَ لَکَ قَوْلاً فَصَدِّقْهُ وَ کَذِّبْهُمْ وَ لاَ تُذِیعَنَّ عَلَیْهِ شَیْئاً تَشِینُهُ بِهِ وَ تَهْدِمُ بِهِ مُرُوءَتَهُ فَتَکُونَ مِنَ اَلَّذِینَ قَالَ اَللَّهُ إِنَّ اَلَّذِینَ یُحِبُّونَ أَنْ تَشِیعَ اَلْفٰاحِشَةُ فِی اَلَّذِینَ آمَنُوا لَهُمْ عَذٰابٌ أَلِیمٌ فِی اَلدُّنْیٰا وَ اَلْآخِرَةِ.» ²

“Ya Muhammad! Ka ƙaryata abin da kunnuwanka da idanunka suka ji ko suka gani game da ɗan’uwanka. Ko da mutane hamsin suka rantse suka ba da shaida a game da ɗan’uwanka, amma shi ya faɗa maka abin da ya saɓa da abin da suka ce, ka gaskata shi, ka ƙaryata su. Kada ka yaɗa wani abu game da shi da zai kunyata shi ko ya ɓata mutuncinsa, domin idan ka yi haka, za ka kasance cikin waɗanda Allah Ya ce: ‘Waɗanda suke son alfasha ta yaɗu a tsakanin muminai, suna da azaba mai raɗaɗi a duniya da Lahira.’”

Saboda haka, kamar yadda hura wuta ke sa ta ƙara ci da yaɗuwa, haka nan yaɗa zunubi, saɓon Allah da duk wani abu da ba ya cikin yardar Allah Maɗaukaki ke sa waɗannan abubuwa su yaɗu a cikin al’umma da duniya, musamman saboda irin damar da kafafen sadarwa na zamani suka samar.

Sakamakon haka, baya ga kunyata mutane da ɓata musu suna, mutane da dama waɗanda a baya ba su da wani sani ko tunani game da irin wannan zunubi na iya saninsa, har ma wasu su aikata shi. A ƙarshe, hakan na iya jefa al’umma cikin lalacewa.

Saboda haka ne Amirul Muminina Ali (A.S) ya yi mana wannan gargaɗi:

«مُذِیعُ اَلْفَاحِشَةِ کَفَاعِلِهَا.» ³

“Mai yaɗa alfasha kamar mai aikata alfasha yake.”

To, idan muka yi la’akari da waɗannan ayoyi da ruwayoyi, me ke faruwa a shafukan sada zumuntarmu a yau?!

Madogara:

1. Suratun Nur, aya ta 19.

2. Wasa’ilush Shi’a, juzu’i na 12, shafi na 295.

3. Ghurar al-Hikam, juzu’i na 1, shafi na 704.

An shirya a Sashen Ilimi da Al’adu na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha